27 Janairu 2016 - 16:01
Mutane 10 sun halaka a harin Chibok

Akalla mutane 10 sun rasu a yayin da wasu sama da 30 suka jikkata sakamakon hare-haren kunar bakin wake da aka kai a wurare uku a garin Chibok na jihar Borno.

Ana zargin 'yan Boko Haram da kaddamar da wadannan hare-haren.

Bayanai sun ce an tayar da bam guda a kasuwar garin da kuma daya a wurin binciken ababen hawa.

"Akalla mutane 10 sun rasu, a yayin da fiye da 30 suka samu raunuka," in ji Ayuba Chibok.

A garin na Chibok ne a 2014 aka sace 'yan mata dalibai su sama da dari biyu, wadanda har yanzu ba aji duriyar galibinsu ba.288